in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ta Kudu ya yi addu'ar neman gafara gabanin babban taron warware rikicin kasar
2017-03-11 12:29:17 cri
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi addu'ar neman gafara yayin wani taron yi wa kasar addu'ar domin samun saukin rikicin kabilanci da take fama da shi sama da shekaru uku da suka gabata.

Addu'ar da ya gudana a jiya Jumma'a, na da nufin samar da kyakkyawan yanayi da nasara, ga babban taron hawan teburin sulhu da shugaban ya kirkiro a watan Disamban bara, domin taimakawa wajen sulhuntawa da hada kan bangarori masu adawa da juna a kasar mai arzikin mai, mai kuma kankantar shekaru.

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da wannan taro, Shugaba Kiir da gwamnatinsa sun ce za su saki 'yan siyasar da ake tsare da su, inda shugaban ya ce a iya saninsa, manyan 'yan siyasa uku ne gwamnatinsa ta tsare.

Daga cikin 'yan siyasar uku da ake tsare da su akwai tsohon gwamnan jihar Wau, Elias Waya Nyipuoch da tsohon mataimakinsa Andrea Dominic, wadanda aka tsare su bisa zargin tunzura rikicin kabilanci a jihar Wau, a watan Yunin 2016 da ya yi sanadin mutuwar mutane 43 tare da raba wasu 12,000 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China