Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya rawaito cewa, mutanen da suka mutu sun hada da kananan yara 3, kana harin saman ya haddasa raunatar mutane da dama, watakila yawan mutane da za su mutu zai karu. Bugu da kari an lalata gidajen fararen hula da dama a sakamakon harin saman.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru suka bayar, an ce, kawancen kasa da kasa ya kai hare-haren sama a wata makaranta da wani masallaci da aka tsugunar da wadanda suka rasa gidajen su a jihar Al-Raqqah a watan da ya gabata, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 77.
A watan Satumban shekarar 2014, kasar Amurka da sauran kasashe suka kafa kawancen kasa da kasa don kai hare-hare ta sama ga kungiyar IS dake kasar Syria da Iraki. A ganin gwamnatin kasar Syria, kawancen ya yi aikin ba tare da samun izni daga kwamitin sulhun MDD ba, kana ta zargi kawancen da kaiwa hare-hare ta sama wadanda suka haddasa mutuwa da raunatar fararen hula da dama. (Zainab)