Sanarwar da ma'aikatar harkokin waje ta bayar ta ce, yadda kasar Amurka ta dauki matakan soji kan sojojin gwamnatin Syria wadanda ke kokarin yakar ta'addanci ba tare da fahimtar ainihin abubuwan da suka faru a lardin Idleb na kasar ta bangaren harba makamai masu guba ba, hari ne ga kasar mai mulkin kanta, kuma matakin zai kara rura wutar rikici tare kuma da lalata huldar da ke tsakanin Rasha da kuma Amurka.
Ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov wanda a halin yanzu ke halartar taron majalisar ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar CIS a Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan, ya ce, wannan matakin da Amurka ta dauka ya tuna wa al'umma yadda kasar da kuma kasashen kawanyenta suka kai hari kasar Iraqi a shekarar 2003 ba tare da samun iznin MDD da kuma isassun abubuwan da ke iya tabbatar da mallakar manyan makaman kare dangi a kasar ba.(Lubabatu)