in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria: an karya lagon kungiyar Boko Haram, yayin da shugabanta ya tsere
2017-03-29 13:31:04 cri
Ministan tsaro na Nijeriya Mansur Dan-Ali, ya ce dakarun kasar sun riga sun yi galaba akan kungiyar Boko Harama, inda a yanzu shugabanta Abubakar Shekau ya tsere.

Mansur Dan-Ali ya ce sojoji sun lalata hedkwatar Kungiyar, amma suna tsammanin shugaban kungiyar ya buya a wani wuri cikin dajin Sambisa, wanda a yanzu dakaru ke kokarin mamayewa.

Ya ce nan bada jimawa ba sojoji dake binciken inda ya ke a dajin, za su kai ga cafke shi.

Rundunar sojin Nijeriya dai ta sanar da mutuwar Shekau har sau biyu a shekarar 2014.

Abubakar Shekau ya sha fitar da faya-fayen bidiyo, inda yake ikirarin ya na raye, tare da barazanar kara kai muggan hare-hare a kasar.

Sai dai, rundunar ta ce an tabbatar da cewa fayafaye ba sahihai ba ne, domin an yi musu gyaran fuska. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China