in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an tsaron sun kama mayakan Boko Haram 3 a Najeriya
2017-02-28 09:19:36 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami'an tsaro sun samu nasarar damke wasu 'yan kasar Chadi su uku da ake zargin suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

Mai magana da yawun sojojin Najeriyar Kanar Sani Usman wanda ya shaidawa manema labaran hakan, ya ce a ranar Lahadi ne sojoji tare da hadin gwiwar 'yan sandan leken asiri suka samu nasarar kame mutanen uku a garin Gobe dake yankin arewa maso gabashin kasar, biyo bayan bayanan asiri da suka samu.

Kanar Usman ya ce, samu maharan da tarin abubuwan fashewa a lokacin da aka kama su, wadanda aka bayyana sunayensu da, Bilal Muhammed Umar da Bashir Muhammed da kuma Muhammed Maigari Abubakar dukkansu 'yan kasar Chadi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutanen suna kokarin kaddamar da wasu hare-hare ne a lokacin da jami'an tsaron suka kama su a maboyarsu da ke Arawa da Mallam Inna a garin na Gombe.

Kakakin sojojin Najeriyar ya ce, binciken baya-bayan sun nuna cewa, 'yan kasashen wajen da aka kama din magoya bayan daya daga bangaren kungiyar ta Boko Haram ce.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China