A jiya Jumma'a ne hukumomi a Nijeriya, suka yi gargdin cewa, wata kungiya dake mubaya'a da kungiyar 'yan tada kayar baya ta Boko Haram, wato Muslim Brotherhood dake jihar Kogi a yankin arewa ta tsakiya, na kokarin mallakar sinadaran hada bam da muggan makamai, da nufin kaddamar da hare-hare a wuraren da suka hada da bankuna da wuraren da ake adana makamai da kuma gidajen yari.
Wata sanarwa da Ministan labarai da al'adu na kasar Lai Muhammad ya fitar, ta ce wasu rahotannin sirri sun bayyana cewa, kungiyar na kokarin fadada ayyukanta, ta hanyar mallakar sinadarai daban-daban na hada bamabamai.
Haka zalika, ya ce rahotannin sun bayyana cewa, kungiyar na kokarin mallakar muggan makamai ciki har da makamin roka.
Ministan ya kara da cewa, 'ya'yan kungiyar na shirin 'yanto 'yan uwansu da aka kama a jihohin Kogi da Kaduna da kuma Abuja babban birnin kasar, ciki har da wani Bilyaminu wanda kwararre ne wajen hada ababan fashewa, da a yanzu haka ke gidan yarin Kuje.
A don haka, Lai Muhammad ya yi kira ga 'yan Nijeriya su rika kula tare da kai rahoton duk wani mutum ko abu da ba su yadda da shi ba ga hukumomin tsaro.( Faiza Mustapha)