in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mayakan Boko Haram sama da 3,000 a Najeriya
2017-02-03 09:18:53 cri
Rahoranni daga Najeriya na cewa, daga watan Janairun zuwa 1 ga watan Fabrairun wannan shekara sojojin Najeriyar da ke aikin kakkabe mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, sun yi nasarar kama mayakan Boko Haram sama da dubu 3, biyo bayan samamen da suka kaddamar a maboyar 'yayan kungiyar da ke dajin Sambisa.

Kwamandan shirin yaki da mayaka na Boko Haram Manjo janar Lucky Irabo wanda ya bayyana hakan ga manema labarin, ya ce, cikin wadanda aka kama akwai 'yan kasashen Chadi 17 sai kuma 9 daga Jamhuriar Nijar.

Yanzu haka dai ana tsare da mayakan da aka kama inda ake yi musu tambayoyi.

Irabo ya kara da cewa,sojojin sun kuma yi nasararkama wasu mutane biyar da aka yi imanin cewa, manyan jagororin kungiyar ce, baya ga wasu tarin makamai da aka kwato yayin samame daban-daban da sojojin suka kaddamar da nufin kakkabe gyauron mayakan na Boko Haram a sassa daban-daban na yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya

Sojojin dai sun samu wadannan nasarori ne tare da hadin gwiwar kungiyoyin 'yan banga da ke yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China