Shugaban rundunar tsaron Nijeriya a Jihar Borno, Ibrahim Abdullahi da ya bayyana haka, ya ce kwamandan kungiyar Boko Haram ne ya ba yaron umarnin shiga wasu kasuwanni domin leken asiri.
Ibrahim Abdullahi ya ce yayin da yaron yake bada bayanai, ya ce an tilasta masa kashe wasu mutane 13 da kungiyar ta yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa, Kungiyar Boko Haram ta kama shi ne shekaru uku da suka gabata, inda aka ajiye shi a wani daji dake garin Kalabalge na jihar Borno.
Har ila yau, yaron ya shaidawa jami'an tsaro cewa, sama da yara 500 da suke kai daya ne kungiyar ta horas a matsayin sojoji. (Fa'iza Mustapha)