Rahoton matsalar abincin da ake fuskanta a fadin duniya da darakta Janar na hukumar samar da abinci ta MDD Jose Graziano da Silva ya fitar, ta ce za a samu karuwar kudin da za a kashe wajen kyautata rayuwar jama'a idan a kan bari yanayin da ake ciki ya kara ta'azzara.
Ya ce ba za a iya hana mutuwar mutane sanadiyyar yunwa ba, amma idan ba a kara inganta ayyuakan ceto, da ba da kariya da kuma inganta rayuwar al'ummomin karkara ba, miliyoyin mutane ne za su ci gaba da kasancewa cikin matsalar rashin abinci.
Rahoton ya ce rikice-rikice a tsakanin al'ummomi ne ke haifar da 9 daga cikin matsalolin jin kai 10 da ake samu, yana mai jadadda alakar da ke akwai tsakanin zaman lafiya da wadatar abinci.
Ya ce a bana, bukatar agajin jin kai da kayayyakin more rayuwa zai kara ta'azzara, la'akari da kasashe hudu da suka hada da Sudan ta Kudu da Somalia da Yeman da Arewa maso gabashin Nijeriya dake fuskantar barazanar fadawa yanayin na yunwa. (Fa'iza Mustapha)