in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi na'am da kara wa'adin shirin baiwa yara kariya a Sudan
2017-04-05 10:30:28 cri
A jiya Talata MDD ta nuna goyon bayanta na kara wa'adin shirin kasar Sudan na baiwa yara kanana kariya daga fuskantar cin zarafi.

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar, ta yabawa irin nasarar da aka cimma a kasar ta Sudan, wajen aiwatar da wannan doka, wanda ake yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da MDD domin kare hakkin yara kanana.

Sanarwar ta kara da cewa, an samu gagarumar nasara game da aiwatar da wannan shirin daga bangaren gwamnatin Sudan, cikin nasarorin da aka cimma akwai batun sakin wasu kananan yara 21 da ake tsare da su bisa alaka da kungiyoyi masu dauke da makamai, kana an tabbatar da yi musu afuwa karkashin dokar yin afuwa ta ofishin shugaban kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China