in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya bukaci a baiwa gaulaye damarsu
2017-04-03 13:19:08 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, yayi kira ga kasashen duniya da su baiwa mutanen dake fama da matsalar gaulanta cikakkiyar dama, domin su ba da tasu gudumowar wajen cigaban al'umma.

Guterres, ya yi wannan roko ne a lokacin bikin wayar da kai game da matsalar masu fama da gaulanta ta kasa da kasa da aka gudanar a jiya Lahadi.

Mista Guterres, ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya gabatar inda ya nuna cewa, doka ta ba da dama ga dukkanin mutanen da suka da matsalar gaulanta a ba su dama daidai wa daida kamar sauran mutane a cikin al'umma.

Ya kuma bukaci a tallafawa mutanen dake fama da wannan matsalar ta gaulanta su yi zabin irin abubuwan da suke so a rayuwar su, kuma a basu yanci kamar kowane mutum, domin su samun makoma mai kyau a rayuwarsu ta nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China