Liu Jieyi, wanda shi ne zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya yi wannan kira ne a lokacin taron kwamitin tsaro na MDD wanda ya gudanar game da nazartar zargin da ake yi na yin amfani da sinadarai masu guba a kasar Syria.
An bada rahoton mutuwar mutane 70, kana wasu 200 kuma sun samu raunuka a wani harin da aka kai ta hanyar amfani da iskar gas kan 'yan tawaye a yankin Idlib dake arewa maso yammacin Syria.
Kasar Sin ta yi Allah wadai da yin amfani da sanadarai masu guba a kowace kasa ta duniya, ko kuma daga kowace irin kungiya ko kuma wani mutum a kowane irin yanayi, Mista Liu ya ce muna yin Allah wadai da kakkausar murya game da kaddamar da hari kan fararen hula.
Ya kara da cewa ya zama wajibi a binciko wadanda ke da alhakin aikata irin wadannan laifuka na yin amfani da sinadarai masu guba don hukunta su.
Liu ya jaddada muhimmancin daukar matakai na siyasa a matsayin sahihiyar hanya ta warware rikicin Syria. (Ahmad Fagam)