'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu Turkawa ma'aikatan kamfanin gine gine na BKS su biyu, daga Otel din da suke zaune a yankin Eket na karamar hukumar Onna a jihar Akwa Ibom dake kudu maso gabashin Najeriya.
Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar 'yan sandan kasar reshen jihar ta Akwa Ibom Chukwu Okechukwu, ya ce an yi garkuwa da mutanen ne su biyu daga Otel din Airstrip a ranar Lahadi, kuma tun daga lokacin ne rundunar 'yan sanda ta tura dakarun ta na musamman masu yaki da satar mutane, da masu yaki da miyagun laifuka yankin, domin tabbatar da an kubutar da Turkawan ba tare da wani lahani ba.
Mr. Okechukwu ya ce kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace mutanen, kuma ba a nemi wani kudin fansa a kan su ba.
Jihar Akwa Ibom mai arzikin mai dai na cikin jahohin dake kan gaba, wajen hada hadar albarkatun mai da iskar gas a tarayyar Najeriya.(Saminu Alhassan)