Osagie Ehanire, shi ne karamin ministan lafiya na Najeriya ya fada a taron manema labarai a Maiduguri cewa, kafa cibiyar na daga cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka na farfado da tunanin mazauna yankunan masu fama da rikice rikice.
Ehanire ya ce kafa cibiyar kula da tunanin mutanen da rikicn Boko Haram din ya shafa na daya daga cikin kudurorin gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari na sake gina wannan yankin.
Ministan ya kara da cewa, za'a tura jami'an kula da lafiya cibiyoyin kiwon lafiyar da aka tanada, ya ce wasu daga cikin jami'an za su bi gida gida domin ba da kulawa ga al'ummomin wadancan yankunan.
Boko Haram ta hallaka mutane sama da 20,000, kana wasu miliay 2.3 sun tsere daga gidajensu daga shekarar 2009. (Ahmad)