Kotun wanda take zamanta a Akure, babban birnin jahar Ondo, ta samu mutanen 7 ne da aikata laifin yin garkuwa da tsohon dan takarar wanda gwamnatin jahar ta shigar da karar.
Haka zalika, ana zargin mutanen da laifin shirya fashi da makami, wadannan su ne biyu da cikin laifukan da ake tuhumar mutanen da aikatawa.
Falae wanda ya kasance tsohon sakataren gwamnatin tarayya, kuma tsohon ministan kudin kasar, an yi garkuwa da shi ne a gidan gonarsa dake kauyen Ilado a kudu maso yammacin birnin Akure na jahar ta Ondo a ranar 21 ga watan Satumbar bara, kafin daga bisani aka sako shi 'yan kwanaki bayan yin garkuwa da shi. (Ahmad Fagam)