Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA, ya shedawa kamfanin dillacin labarai na Xinhua cewa, jami'an tsaron sun tsare mata 'yan kunar bakin waken ne, inda suka dakile harin da suka kuduri aniyar kaddamarwa a kusa da jami'ar Maiduguri.
Kakakin na NEMA ya ce ba'a samu hasarar rayuka ko jikkata ba, bayan matan biyu 'yan kunar bakin waken da suka mutu nan take.
Wannan yunkurin kai harin ya zo ne kwanaki biyu bayan wani harin da aka kai wani masallaci a birnin na Maiduguri. Harin ya raunata mutane hudu a karshen mako, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar.
Birnin na Maiduguri inda a can aka kyankyashe kungiyar ta Boko Haram, kuma birnin ya kasance a matsayin hedkwatar mayakan Boko Haram a shekaru da dama, kafin daga bisani dakarun Najeriya suka fatattaki mayakan daga babbar maboyarsu a watan Disambar bara.
Hare haren mayakan na Boko Haram, ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 20,000 kuma ya raba mutane sama da miliayn 2 da dubu 300 da gidajensu daga shekarar 2009 zuwa yanzu. (Ahmad Fagam)