Kafin haka kuwa, kungiyoyin sun shafe tsawon mintina 90 ko wacce tana da kwallo 3 a raga.
Wellington Silva na Fluminense ne ya fara daga ragar Flamengo a mintuna 4 da take wasa, kafin daga bisani William da Everton na Flamengo su kara kwallaye 2.
Sa'an nan kwallaye 2 da Henrique Dourado, da Lucas suka ci Fuminense sun kusan sanyawa a tashi wasan 3 da 2, sai dai daga bisani dan wasan Flamengo Paolo Guerrero, ya samu nasarar jefa kwallo ta 3 a raga cikin mintuna 84, wanda hakan ya sanya kungiyoyin 2 tashi canjaras bayan kammala wasan cikin mintuna 90.
Wannan ya kasance karo na 10 da Fluminense ta lashe kofin Guanabara karkashin tsarin gasar kwararrun kuloflikan wasan kwallon kafa ta kasar Brazil, sai dai guda 8 daga cikin kofunan ta same su ne kafin shekarar 1993.(Bello Wang)