in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar ya zama zakaran kwallon kafa na duniya, inji kociyan Brazil
2017-04-13 09:07:35 cri
An bayyana dan wasan kungiyar kwallon kafan Barcelona Neymar a matsayin zakaran kwallon kafa na duniya a wannan shekarar ta 2017, kamar yadda mai horas da babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta Brazil Tite ya tabbatar.

Sai dai kamar yadda tsohon jami'in kungiyar wasan Corinthians ya ce, lamarin zai kasance tamkar an yi azarbabi ne, idan aka yi saurin bayyana dan wasan mai shekaru 25 a duniya da cewa ya sha gaban zakarun wasan kwallom kafa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, bayan kammala zabar gwarazan yan wasan kwallon kafa da bayar da lambobin yabo.

Tite ya tabbatarwa gidan Radiyon Bandeirantes a Juma'ar data gabata cewa, Neymar yana kan ganiyarsa a halin yanzu, kuma kwatantashi da Cristiano Ronaldo da Messi tamkar rashin adalci ne.

Tite ya kara da cewa, sun kasance masu mabanbantan shekaru. A shekaru 10 da suka gabata bai kasance fitaccen dan kwallon duniya ba. Yace shi a ra'ayinsa dan wasan kwallon kafa da yafi kowanne a duniya shine Messi. Amma cikin watanni 4 da suka gabata, dan wasan kwallon kafan da yafi kowanne a duniya shine Neymar.

Tun bayan fara gasannin kakar wasa ta 2016-17, Neymar, ya kasance a sahun gaba a dukkanin kungiyoyin wasannin kwallon kafan da ya taka musu leda, tun daga farkon fara wasannin na wannan shekara.

Maki mafi girma da ya samu shine na rawar da ya taka a lokacin wasannin zakarun nahiyar turai na UEFA Champions League a ranar 16 ga watan jiya, a lokacin da Barcelona suka tashi da ci 6-5 a wasan inda ta zara kwallaye biyu a lokacin da ya rage mintoci 5 a tashi daga wasan zagaye na biyu a Camp Nou.

Neymar ya kuma zarawa Brazil kwallaye a lokacin wasanta da Uruguay da kuma Paraguay a watan jiya wanda wannan nasarar ta baiwa kungiyar wasan Selecao samun damar zama kasa ta farko da zata shiga wasan kwallon kafa na duniya a badi, bayan da haye a wasannin share fagen.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China