in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kociyan Brazil Tite yana rangadi a Turai
2017-02-15 16:58:12 cri
Kociyan kasar Brazil Tite da yan tawagarsa sun fara wani rangadi a turai domin duba yadda yan babbar kungiyar wasa ta kasar da wadan da aka zaba suke gudanar da ayyukansu.

Daga cikin wasannin da Tite da babban mataimakinsa Edu Gasper zasu duba, zasu halarci Paris Saint-Germain inda zasu kalli yadda za'a murza leda tsakanin Barcelona da Bayern Munich da kuma Arsenal a wasan cin kofin kwararru na Champions League.

Gaspar, ya fada cikin wata sanarwar da aka wallafa a shafin internet na kungiyar wasan kwallon kafan kasar Brazil cewa, abune mai kyau su dinga bibiyar yadda yan wasansu ke taka leda.

A cikin sanarwar yace, yana da tabbacin wannan aikin da suke yi zai kara inganta ayyukan da suke yi, da kuma inganta tattaunawar da suke yi da jami'an kungiyoyin wasan na turai.

Sauran mambobin na tawagar Tite zasu kalli wasanninsu sun hada da Real Madrid, Valencia, Juventus, Porto da kuma wasan Inter Milan nan da kwanaki 6 masu zuwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China