in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Leverkusen ta sallami babban kocinta Schmidt
2017-03-07 16:08:22 cri
A tsarin gasar kwallon kafa ta kasar Jamus Bundesliga, Bayer Leverkusen ta sanar da sallamar babban kocin kulob din Roger Schmidt. Kulob din Bayer Leverkusen ta dauki wannan mataki ne bayan da Borussia Dotmund ta lashe ta da ci 6 da 2, a wasan karshen makon da ya gabata.

Hakan ya kasance karo na 2 a jere da kungiyar ta hadu da rashinn nasara a wasannin da ta buga, kuma matakin ya sauke matsayin kungiyar zuwa ta 10 a teburin Bundesliga.

Roger Schmidt, mai shekaru 49 a duniya, ya tsallake zuwa Leverkusen ne a watan Afrilun shekarar 2014, daga FC Salzburg. Karkashin jagorancinsa, kungiyar ta kai ga zagayen rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai har karo 3. A kuma cikin wasanni 125 da kungiyar ta buga a shekaru 3 da suka wuce, kungiyar ta ci nasarar wasanni 62, da yin kunnen doki a wasanni 27, yayin da kuma ta yi rashin nasara a sauran wasanni 36.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China