in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jimamin tsohon kwociyan kasar Ghana
2017-02-15 17:15:09 cri
Hukumar kwallon kafar kasar Ghana (GFA), ta sanar da rasuwar tsohon kocin kasar Sam Arday. Mr. Arday wanda ake wa lakabi da "Mai tarin dabaru ", ya rasu ne a birnin Accra ranar Lahadin da ta gabata, bayan wata gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 71 da haihuwa.

Kafin rasuwar sa Mr. Arday ta kasance darakta a cibiyar horas da 'yan wasa ta Afirka ta yamma reshen kasar ta Ghana. Ya kuma taba kasancewa kociya ga kungiyar Black Meteors, kungiyar kasar Ghana da ta lashe lambar tagulla a gasar kwallon kafar Olympic da aka yi a shekarar 1992 a birnin Barcelonan kasar Sifaniya. Wanda hakan ya baiwa kasar damar kasancewa ta farko a Afirka da ta lashe lambar yabo a gasar kwallon kafar Olympics.

Daga nan kuma ya jagoranci kungiyar matasa 'yan kasa da shekaru 17 wato Black Starlets, wadda ta lashe gasar hukumar FIFA ta shekarar 1995 a Ecuador. Har wa yau ya shugabanci kungiyar Black Stars a shekarun 1996 da 1997, da kuma 2004.

Hukumar ta GFA ta ce daukacin masoya kwallon kafa da mahukuntan ta, sun kadu matuka da jin rasuwar Mr. Arday, tana kuma mika sakon ta'aziyyar sa, ga iyalai da 'yan uwan sa, kamar dai yadda wata sanarwar hukumar ta bayyana.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo-Addo, ya gabatar da sakon sa na ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwan marigayi Arday, yana mai cewa Ghana ta yi rashin mai horas da 'yan wasa na hakika, wanda daya ne daga kociya mafiya hazaka da kasar ta taba samu.

Cikin sakon tweeter da shugaban na Ghana ya fitar, ya ce yayi matukar kaduwa da jin rasuwar wannan gwarzo a fagen kwallon kafar kasar sa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China