in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kara gaba a jadawalin hukumar FIFA
2017-02-15 17:17:11 cri

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta daga da matakai tara zuwa gaba, a jerin jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, inda ta kai mataki na 41 daga na 50 da take a cikin watan da ya gabata.

Jadawalin na watan Fabreru, da hukumar FIFA ta wallafa a shafinta na Website, ya nuna cewa, har yanzu Najeriya na rike da matsayinta na 7 a nahiyar Afrika, duk da gazawarta na shiga gasar cin kofin Afrika da aka kammala a ranar Lahadi da ta gabata, da Kungiyar kwallon kafar Kamaru, Indomitable Lions ta lashe.

Sabon jadawalin na FIFA ya nuna cewa, Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta samu maki dari shida da tamanin da shida, wanda ya dara maki dari shida da goma sha tara da ta samu a watan Junairu. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China