A kuma wannan rana, shugaban cibiyar dake kula da aikin warware ricikin Syria ta kasar Rasha dake kasar Syria Sergey Kuralenko, ya bayyana cewa, kiran da mahukuntan Rasha suka yi domin ganin an shimfida yanayin kwanciyar hankali a kasar Syria, ya sa hukumar tsaron kasa yin kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa, da su dakatar da musayar wuta tsakaninsu, su kuma kawar da alaka da kungiyar ta'addanci ta Jabhatal-Nusra, duba da cewa sojojin kasar ta Rasha za su ci gaba da kai hari ta sama, kan yankunan dake karkashin ikon 'yan ta'addan. (Maryam)