in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tinkarar sauyin yanayi ya samar da dama ga kasa da kasa wajen bunkasa kasa ba tare da gurbata yanayi ba
2017-04-11 20:35:04 cri
Wakilin Sin na musamman mai kula da harkokin sauyin yanayi Xie Zhenhua ya bayyana a yau Talata cewa, sauyin yanayi kalubale ne da dukkan Bil Adama ke fuskanta, ana kuma bukatar dukkan bangarorin da suka daddale yarjejeniyar tinkarar matsalar sauyin yanayi, da su yi kokari tare wajen tinkarar wannan kalubale.

Mr. Xie ya ce idan wata kasa ta kasa cika alkawarin da ta dauka, hakan zai haifar da karin matsin lamba ga sauran kasashen dake na su kokarin. A daya bangaren na daban kuma, tinkarar sauyin yanayi na samar da dama ga kasashe a fannin bunkasa yankunan su, ba tare da gurbata yanayi ba.

Xie Zhenhua ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru, na taron ministoci na karo na 24, wanda ya kushi kasashen Sin, da Indiya, da Brazil, da Afirka ta Kudu, game da tinkarar sauyin yanayi. Ya ce yana fatan kasashe masu ci gaban tattalin arziki, za su cika alkawarinsu na samar da kudi har dala biliyan 100, ga kasashe masu tasowa a kowace shekara, nan zuwa shekarar 2020.

Yanzu haka dai kasashen hudu manya dake halartar taron, da ma sauran kasashe masu tasowa, na kokarin gudanar da hadin gwiwa da juna game da tinkarar sauyin yanayi, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu a fannin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China