in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar taswirar da MDD ta fitar za ta taimaka wajen aiwatar da shirin kariyar hamadar Afirka
2016-11-17 09:17:48 cri

An kaddamar da sabuwar taswirar MDD, wadda za ta tallafawa aniyar da ake da ita, ta kange yankunan nahiyar Afirka daga barazanar kwararar Hamada.

Mataimakin kakakin MDDr Farhan Haq ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, yana mai cewa, an kaddamar da wannan taswira ne a taron sauyin yanayi na duniya dake gudana yanzu haka a birnin Marrakesh na kasar Morocco.

Mr. Haq ya ce, taswirar ta ayyana yadda za a tabbatar da cimma nasarar dashen itatuwa a yankunan nahiyar Afirka mafiya fama da fari, a wani mataki na dakile kwararar Hamadar.

Masana dai na cewa, akwai bukatar daukar matakai daban daban, idan har ana da burin cimma nasarar kafuwar wannan ganuwa ta shuke shuke, wadda za ta karade yankunan arewaci, da na Hamada, dama gabashin nahiyar ta Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China