Shugaban babban taron sauyin yanayi na MDD na Marrakech Salaheddine Mezouar ya ce, yana fatan yin kokari tare da kasar Sin wajen inganta hadin kai kan batun sauyin yanayi tsakanin kasashe masu tasowa.
Shugaban babban taron ya bayyana haka ne a yayin da yake hira tare da manema labaru na kamfanin Xinhua a jiya Asabar, inda ya kara da cewa, irin wannan hadin kai na da muhimmanci kwarai ga kasashe masu tasowa, tsarin hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa yana amfana wa kasashe masu tasowa wajen neman hanyar tinkarar sauyin yanayi, yana fatan yin kokari tare da kasar Sin don karfafa irin wannan hadin kai.
Baya ga haka, a matsayinsa na ministan harkokin diplomasiyya da hadin kai na kasar Morocco, Salaheddine Mezouar ya nuna yabo ga kasar Sin sakamakon goyon baya da ta nuna wa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka wajen neman hanyar samun dauwamamman ci gaba, a ganinsa, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a kai. (Bilkisu)