in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD na fatan ganin an koma tattauna rikicin Syria nan ba da dadewa ba
2017-03-11 12:24:00 cri
A jiya Jumma'a, kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da kokarin da Manzon musammam na MDD a Syria Staffan de Mistura ke yi na shiga tsakani domin sulhunta bangarorin da ke adawa da juna a Syria.

Kwamitin ya kuma yi fatan ganin an dawo tattauna yadda za a warware rikicin da a wannan wata ke shiga shekara na bakwai, nan ba da dadewa ba.

Wata sanarwar da kwamitin mai mambobin kasashe 15 ya fitar, ta ce kwamitin ya yi maraba da kammala wani zagaye na tattaunawar da MDD ta taimakawa samarwa, da ya gudana a ranar 3 ga watan nan da muke ciki a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Sanarwar ta kara da cewa, mambobin kwamitin na sa ran ganin an koma teburin na sulhu nan bada dadewa ba, suna masu karfafawa bangarorin na Syria gwiwar komawa da kyakkyawar fata, tare da tattaunawa ba tare da gindaya wasu sharudai ba, kan batutuwan da manzon musammam na MDD ya tsara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China