Shugaban likitoci masu binciken musababbin barkewar cututtuka a cikin al'umma na jihar Akwa Ibom, Aniekeme Uwah, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, gwamnatin jihar ta umarci ma'aikatan kiwon lafiyar al'ummma, su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don dakile yaduwar barkewar cutar.
Aniekeme Uwah ya ce duk da ba a samu bullar cutar a jihar ba, an dauki matakan yaki da ita, ciki har da samar da kibabbiyar cibiya ta bada daukin gaggawa.
An yi hasashen samun barkewar cutar dake bulla a lokacin zafi a Nijeriya, la'akari da yankin da kasar take da kuma yanayi da ake samu na sanyi da daddare, da iska mai kura da kuma zafi.
Masana dai sun alakanta ta'azzara cutar da karancin tsaftar jiki da na muhalli da yawan al'umma da kuma canfi.
Gwammnatin Nijeriya dai ta tura ayarin likitoci masu binciken musababbin barkewar cututtuka da allurar ragakafi zuwa yankunan da cutar ta bulla domin dakile yaduwarta.
Rigakafi dai, shi ne muhimmiyar hanya ta takaita cutar, inda tuni cikin makon da ya gabata, aka fara bada allurar rigakafin tare da kan al'umma game da cutar. (Fa'iza Mustapha)