in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta fara yin rijistar masu kada kuri'a gabanin zaben 2019
2017-04-07 09:56:26 cri
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar a jiya Alhamis cewa, za ta fara aikin ci gaba da yin rijistar masu kada kuri'a a wannan watan na Afrilu kuma za a gudanar da shirin kamar yadda ta tsara.

Shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu, ya shedawa manema labarai a Abuja cewa, ana ci gaba da gudanar da shirye shirye da suka kamata domin fara aikin cikin nasara kamar yadda aka tsara tun da farko.

Yakubu ya ce za'a gudanar da aikin ne a dukkan kananan hukumomin kasar 774.

Ya ce suna ci gaba da tuntubar kwamishinonin zabe na jahohin kasar domin sanin adadin na'urorin da ake bukata da kuma wuraren da za a gudanar da ayyukan.

A cewarsa wannan shirin zai ci gaba da gudana har ma bayan kammala manyan zabukan kasar na shekarar 2019. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China