Ya shedawa gidan talabijin na CNN cewa, ya gwada ta a cikin ruwa, kuma mutane da yawa sun yi mamakin yadda take iya tafiya a cikin ruwa da kuma a doron kasa.
Duroyaije wanda ake yi wa inkiya da "Kenny jet", wanda ya yi tafiyar mil 84 kwatankwacin kilomita 135 daga hanyar Legas zuwa Ibadan a motar tasa wadda ba a saba ganin irinta ba, kuma yana iya yin tafiyar kilomita 120 a cikin sa'a guda a kan titi, kana yana tafiyar nisan gaba 6 a cikin teku.
Mutumin mai shekaru 46 a duniya ya ce, ya dade yana gwada wannan basira tasa wajen kera motar mai tashi sama, kuma ya hada samfurin motar har guda 4 daga cikin tarkacen kayayyakin da yake samuwa kamar allon yin rubutu na na'urar kwamfuta, da karafunan mashin mai kafa 3, da wasu tarkacen robobi wanda yake tsinta a wuraren jibge shara dake kusa da inda yake aikin nasa a Legas.
Bayan da ya zauna a kan kujerar motar da ya kera, Dorojaiye ya ce yana kokarin kammala shirin da yake yi, kuma ya ce yana fata wata rana motar za ta iya tashi sama. (Ahmad Fagam)