in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin kwato 'yan tawayen da suka makala a yankin Barada na Syria
2017-01-20 10:04:02 cri
Wata tawagar MDD da mambobin kwamitin da ke sansantawa sun shiga kwarin Barada dake yankin arewa maso yammacin birnin Damascus na kasar Syria, a yunkurin ganin an kwashe 'yan tawayen da suka makale a yankin mai arzikin ruwa.

Wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin cewa, sai da aka cimma wata yarjejeniya kafin tawagar ta samu izinin shiga yankin. Majiyar ta kara da cewa, yarjejeniyar za ta taimaka wajen kawo karshen takaddamar yankin ruwan Ain Fijeh wanda aka yi kiyasin cewa, yana samarwa mazauna babban birnin Syria sama da miliyan biyar ruwan sha.

Rahotannin na cewa, tun a ranar 22 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ce, aka katse hanyar samar da ruwan, sakamakon fadan da ya barke a yankin, inda sassan da ke gwabza fadan ke zargin juna da haddasa matsalar ruwan da ake fuskanta a birnin Damascus.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta kasar Syria mai hedkwata a birnin Landan, ta ce mayakan saman Syria suna kaiwa 'yan tawaye da ke yankin hare-hare ta sama.

A halin da ake ciki kuma, rahotanni na cewa, 'yan tawayen Nusra sun fara kona gidaje a yankin Ain Fijeh, a matsayin ramuwar gayya dangane da matakan da sojoji suka daka na kwace yankin da ke hannunsu.

Wannan lamari na zuwa ne bayan cimma wata yarjejeniya a ranar 11 ga watan Janairu a yankin, wadda za ta baiwa gwamnati damar warware matsalar yankin, kana daga bisani a kai ga kwashe kungiyoyin 'yan tawayen dake yankin zuwa lardin Idlib. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China