in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Tibet ya sake amincewa da karin wasu kwararrun masana magungunan gargajiya
2017-04-11 10:06:59 cri
Kimanin kwararrun masana magungunan gargajiya na yankin Tibet 20 ne aka amince da su a hukumance, a yayin da aka gudanar da bikin kammala shirin horas da su a jiya Litinin a wani mataki na bunkasa wannan fanni.

An amince da kwararrun masana magungunan gargajiyar na Tibet ne a Lhasa, babban birnin yankin, inda kawo yanzu jimillar kwararrun masana magungunan gargajiyar ya karu zuwa 72. Biyu daga cikin wadanda aka amince da su din sun samu shaidar karatun digiri na 3 wato doctorate degree, yayin da 8 kuma suka samu shaidar karatun digiri na biyu wato masters degree.

Karkashin wannan shirin, dole ne kwararrun su halarci wani aikin ba da horo na tsawon shekaru 3 tare da fitattaccen masanin magungunan gargajiya na Tibet.

Cering Samzhub, ya yabawa wannan shirin. Inda ya bayyana cewa ya koyi abubuwa masu yawa karkashin koyarwar malaminsa.

Maganin na Tibet mai suna Sowa Rigpa, an jima ana amfani da shi wajen magance cututtuka iri daban daban sama da shekaru 3,800 da suka gabata. Maganin ya samo asali ne daga tsarin gargajiya na kasashen Sin, Indiya da kasashen Larabawa, kuma galibi ana amfani da su ne a yankunan Tibet da Himalaya. Ana amfani ne da wasu ganyaye, ma'adanai a wasu lokutan har ma da wasu nau'i kan kwari da dabbobi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China