in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tsarin sufuri na dukkan fannoni a jihar Tibet ta kasar Sin
2017-01-13 11:06:48 cri

Rahoto daga jihar Tibet mai zaman kanta na kasar Sin ya ce, jimillar tsawon hanyoyin zirga-zirgar motoci da aka shimfida a jihar ta zarta kilomita dubu 82. Haka kuma, yawan filayen jiragen saman da ake amfani da su a yanzu, ya kai biyar. Har ila yau, manyan layukan dogo biyu a Tibet suna aiki yadda ya kamata, wato layin dogon da ya hada Qinghai da Tibet, gami da layin dogon da ya hada Lhasa da Shigatse, al'amarin da ya tabbatar da cewa, an kafa wani ingantaccen tsari da ya kunshi dukkan fannonin sufuri a Tibet.

Wani jami'i na kwamitin neman ci gaba da yin kwaskwarima na jihar Tibet Jiang Taiqiang cewa ya yi, harkokin sufurin jiragen sama na fasinja na bunkasa cikin sauri, inda ya ce adadin hanyoyin sufurin jiragen sama na gida da na waje ya kai 71, haka kuma jiragen sama daga birane 41 ne za su iya zuwa Tibet.

A shekarar da ta shude wato 2016, yawan sauka da tashin jiragen sama a Tibet ya kai dubu 39, inda aka yi jigilar fasinjojin da adadinsu ya wuce miliyan 4.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China