in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala wasu shirye shirye na lura da muhalli a yankin Tibet
2017-02-08 09:25:17 cri
Mahukuntan yankin Tibet mai cin gashin kansa dake kudu maso yammacin kasar Sin, sun ce yanzu haka yankin na da cikakken tsarin kula da muhalli, wanda ke kare ruwa da iska da ingancin kasa.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin shugaban hukumar kula da muhalli a yankin na Tibet Cering Yangzom, ya ce yanzu haka an kafa na'urorin lura da ingancin iska na zamani 23 a birane daban daban, da kuma daura da layin dogo na Qinghai zuwa Tibet.

Kaza lika an zabi wasu tashoshi 194 na lura da ruwa, da kuma wasu 84 da lura da iska, sai kuma wasu 110 domin kula da ruwan sha domin al'ummar yankin.

Tibet din yanki ne mai tudu, yana kuma cikin yankuna mafiya tsaftar muhalli a dukkanin fadin duniya. Mahukuntansa sun kafa dokoki wadanda ke yaki da amfani da makamashi fiye da kima, da fitar da gurbatacciyar iska, da sauran matakai da ka iya jirkita kyakkkyawan yanayi na muhalli. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China