Ya kara da cewa ya samu wannan bunkasa ne ta harkokin kasuwanci, sufuri da kamfanonin fasahar zamani, amma ba ta kakabawa cinikayya haraji mai tsauri ba.
A cewar Hu Suhua, shugaban ofishin hukumar dake tattara haraji na yankin, habakar tattalin arzikin yankin ne ya kai shi ga samun karin kudaden haraji.
Hu Suhua ya kara da cewa, a cikin shekarar da ta gabata, ma'aunin tattalin arzikin yankin na GDP ya kai Yuan biliyan 114.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 16.5, inda ya ce ya karu da kashi 11.5 a kan na shekarar 2015.
Har ila yau, ya ce, shekaru ashirin da hudu a jere ke nan, da yankin ke samun bunkasar tattalin arzikinta a kowace shekara. (Fa'iza Mustapha)