Kudaden shiga da yawon bude ido ya janyo a tsawon farkon watanni tara sun karu da kashi 25.9 cikin 100 bisa shekara daya domin cimma kudin Yuan biliyan 28.7 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 4.25, a cewar kwamitin yawon bude da cigaba na yankin.
A yayin bikin Shoton ko sallar kindirmo, wani babban bikin shekara shekara da ya gudana a ranar 1 zuwa 7 ga watan Satumba, birnin Lhassa ya karbi masu yawon bude ido fiye da miliyan biyu, wanda ya karu da kashi 17.4 cikin 100 bisa shekara guda. A cewar shirin cigaba na shekaru biyar (2016-2020) karo na 13 na yankin, Tibet za ta karbi masu yawon shakatawa fiye da miliyan 30 a shekarar 2020, tare da samun kudaden shiga daga bangaren yawon bude ido da za su zarce Yuan biliyan 55. (Maman Ada)