A Talatar nan ne firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke ziyarar aiki a kasar New Zealand, tare da takwaransa na kasar Bill English, suka halarci wata liyafa tare da gabatar da jawabi a birnin Oakland, taron da ya samu halartar al'ummar kasar fiye da dari 5 daga sassa daban daban.
A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka, kan manufarta ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, kuma ba za ta rufe kofarta ko kadan ba. Kaza lika tana maraba da dukkan shirye-shiryen cinikayya cikin 'yanci, wadanda za su yi amfani wajen raya tattalin arzikin shiyya-shiyya baki daya. (Tasallah Yuan)