A yayin ganawar tasu, firaminista Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana sa kaimi ga kamfanonin kasar da su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da jihar New South Wales, musamman ma a fannonin habaka harkokin dake shafar makamashi, ayyukan gona da kiwon dabbobi, sha'anin kudi da kuma raya harkokin kimiyya da fasaha da dai sauransu, ta yadda za a iya kyautata ma'amala da hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin biyu kan harkokin tattalin arziki da cinikayya, zuba jari, al'adu, ilmi da yawon shakatawa da dai sauransu. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje.
A nasa bangaren, gwamna Berejiklian ya ce, ana maraba da zuwan karin kamfanonin kasar Sin a jihar New South Wales domin su zuba jari a jiharsa. (Maryam)