in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta ranci kudi daga kasar Sin don kammala aikin gina layin dogo
2017-03-28 09:10:05 cri
Gwamnatin Najeriya ta shirya karbar bashin dala biliyan 6.1 daga bankin Exim na kasar Sin, domin amfani da kudaden wajen kammala aikin gina layin dogo nan da shekara ta 2019.

Ministan surufin kasar Rotimi Amaechi, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake kare kasafin kudin kasar na shekarar 2017 a jiya Litinin a gaban majalisar dokokin kasar a Abuja, fadar mulkin kasar.

Amaechi, yace, gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar gina layin dogo daga Lagos zuwa Ibadan, da Kano zuwa Kaduna, da kuma kashi na farko na gina layin dogon daga Legas zuwa Calabar wanda ke kunshe cikin kasafin kudin kasar na shekarar ta 2017.

Ministan ya shedawa 'yan majalisar kasar cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na sake duba ayyukan gina layin dogo da gwamnatocin da suka shude suka bayar, kuma ana son a kammala aikin nasu ne kafin watan Disambar shekarar 2019.

Amaechi yace, akwai bukatar kammala ayyukan gina layin dogon bisa la'akari da irin alfanun da suke da shi ta fuskar cigaban tattalin arziki da kuma cin gajiyar da 'yan kasar za su samu daga wadannan muhimman ayyuykan.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China