in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Borno: Hare haren kunar bakin wake ya hallaka mutane 4 a sansanin 'yan gudun hijira
2017-03-22 19:42:55 cri

A kalla mutane 4 ne aka tabbatar sun rasa rayukan su, kana wasu 18 suka jikkata, yayin wani harin kunar bakin wake da ya auku a sansanin 'yan gudun hijira dake wajen birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno Damian Chukwu, an ji karar wasu fashewa biyu da asubahin yau Labara, a wani sansanin 'yan gudun hijira dake kusa da birnin na Maiduguri, kaza lika wani abu ya fashe kusa da wani wurin gyaran motoci dake birnin.

Mr. Chukwu ya ce ana zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kitsa wadannan hare hare.

Shi ma a nasa bangare, jami'in tsare tsare na sansanin 'yan gudun hijirar da lamarin ya auku Tijani Lumani, ya ce tagwayen fashewar sun haifar da gobara, wadda ta kone wasu tantuna masu yawa. Ya ce mai yiwuwa ne adadin wadanda su rasa rayukan su ya karu, a gabar da ake ci gaba da aikin ceto, na rayukan wadanda lamarin ya rutsa da su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China