Cikin wata sanarwa, wani jami'in rundunar sojin ruwan Nijeriya Capt. Suleiman Dahun, ya ce manufar atisayen ita ce, inganta kwazon kasashen dake mashigin ruwan Guinea da na yammacin Africa, ta yadda za su iya murkushe ayyukan bata gari a tekuna.
Ya ce za a gudanar da atisayen ne a matakai daban-daban a tekunan dake kasashen da suka shiga atisayen, yana mai cewa kasashe 30 ne za su shiga cikin shirin a bana.
Jami'in sojin ruwan ya ce an shirya fara atisayen a Nijeriya ne, daga yau Juma'a 24 ga watan Maris zuwa Talata 28.
A cewarsa, yayin atisayen za a yi amfani da jiragen ruwa uku da jirgi mai saukar ungulu mallakar rundunar sojin ruwan Nijeriya, sai kuma jirgin ruwan sojin Faransa guda daya, wanda zai isa tekun Nijeria daga Kamaru.
Ya kara da cewa, atisayen na da nufin nuna laifukan cikin teku da suka faru a baya, inda wani jirgin ruwa da aka sace zai wuce daga wata iyaka zuwa wata. (Fa'iza Mustapha)