A daidai lokacin da wata sabuwar zanga-zangar kin jinin baki ta barke a wasu garuruwa na kasar, Jacob Zuma ya ce galibin bakin da ke zaune a kasar suna kiyaye doka da oda, sannan suna bada gudunmuwa ga habakar tattalin arzikin kasar.
A jawabin nasa na jiya, ya ce kuskure ne yi wa bakin daurin goro, inda ake alakantasu da safarar miyagun kwayoyi ko na bil'adama.
Sai dai, ya ce al'ummar kasar a yankuna daban-daban sun damu matuka da laifukan da ake aikatawa, wadanda ke tada hankalin al'ummomi.
A farkon watan nan ne zanga-zangar kin jinin baki ya barke a Pretoria ta yamma da kuma Rosenttenville.
Haka zalika al'amura na kara tsanin ta wasu bangarori, ciki har da musayar kalmomin batanci da na barazana a shafukan intanet.
Jacob Zuma ya yi suka da kakausar murya, kan duk wani nau'i na zanga-zanga, ya na mai kira da baki a kasar su kara hakuri, su kuma guji aikata laifuka, sannan, su yi aiki da hukumomin da suka dace domin tabbatar da hukunta wadanda ke aikata laifuka. ( Fa'iza Mustapha)