Kafin ya tashi zuwa birnin Beijing, don halartar shawarwarin tattalin arziki da manyan tsare-tsare zagaye na 8 tsakanin Sin da Amurka, Mr. Lew ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka manyan kasashe ne guda biyu dake sahun gaba a fannin tattalin arziki a duniya, wadanda kuma suke yin babban tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Lew ya ce, ko da yake saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya ragu, duk da haka harkokin sayayya da bada hidima na ci gaba da bunkasa a kasar, wadanda za su kara kawo dama ga kamfanonin kasar Amurka. A hannu guda kuma Amurka za ta ci gaba da sa kaimi ga Sin, wajen bude kasuwannin ta, tare kuma da samar da yanayin takara mai adalci ga kamfanonin kasashen waje.
Haka zalika, Lew ya bayyana cewa kasar Sin na samun babban ci gaba a fannonin tabbatar da ikon mallakar ilimi, da kudin musaya na RMB da sauransu. Kana kasar ta cika alkawarinta na bin tsarin kudin musaya bisa kasuwa. Kuma Amurka za ta ci gaba da lura da manufofin kudin musaya na kasar ta Sin. (Zainab)