Staffan de Mistura ya kara da cewa, bisa aikin shiga tsakani da MDD ta yi, gwamnatin kasar Syria da wakilan jam'iyyar adawa da gwamnati, sun amince da fara tattaunawa kan daftarin da ya kunshi wasu batutuwa hudu da suka hada da kafa gwamnatin hadin gwiwa da gyara tsarin mulkin kasa da sake gudanar da babban zaben shugaban kasa da kuma yaki da ta'addanci.
Yayin zaman na wannan karon, ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, amma a zagaye na shida na tattaunawar da za a yi a nan gaba, bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da tattaunawar neman sulhu a tsakaninsu.
Mr. Mistura ya ce a cikin mako mai zuwa, zai je birnin New York, domin yi wa babban magatakardan MDD da kuma kwamitin sulhu na Majalisar bayani game da sakamakon taron da aka kammala, sannan, zai shirya lokacin da za a fara zagaye na shida na tattaunawar , yana mai cewa, a halin yanzu, bangarorin da tattaunawar ta shafa na sa ran sake hawa teburin na sulhu.
Bugu da kari, yayin taron, Mr. Mistura ya jadadda bukatar bangarori daban-daban da abin ya shafa, su zurfafa tattaunawa a tsakaninsu, kan yadda za a aiwatar da kunshin wancan daftari mai batutuwa hudu, ta yadda za a shiryawa taron neman sulhu, zagaye na gaba. (Maryam)