Kakakin hukumar kula da gidajen yarin Francis Enobore, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua cewa, hukumar ta tona rijiyoyin burtsatsai da dama a bara, sannan ta zuba jari mai yawa a fannin kiwon kifi domin farfado da gonakin hukumar.
Enobore ya ce an tona rijiyoyin burtsasan ne domin noman rani a lokacin zafi dama cikin shekara baki daya.
Rahotanni sun ce akwai yuwar nauyin ciyar da fursunonin ne ya kai hukumar ga yanke shawarar tura fursunonin gonakinta, domin noman abincin da za a ciyar da su.
A baya-bayan nan ne shugabancin hukumar ya farfado da yanayin gonaki mallakar hukumar a fadin kasar dake cikin mawuyacin hali, da nufin samar da abincin da za a ciyar da fursunonin.
Rahoton ya kara da cewa, cikin jimilar fursunonin dake gidajen yarin, kimanin 21,903 ne aka yankewa hukunci, yayin da 46, 351 ke jiran shari'a. (Fa'iza Mustapha)