in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Nijeriya ta amince da cike gibin kasafin kudin 2016
2017-03-23 10:22:45 cri
Majalisar dattijan Nijeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Muhammadu Buhari, ta yin amfani da lamunin dala miliyan 500 daga kasuwar hannun jari ta duniya, domin cike gibin kasafin kudin 2016.

Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo wanda ya rike mukamin shugaban kasar ne, ya aike wasikar ga majalisar a ranar 15 ga watan nan, yana mai neman amincewarta don amfani da kudin wajen cike gibin.

Osinbajo ya ce matakin ya biyo bayan bukatar karbar sabon rance domin aiwatar da kunshin kasafin.

Daukacin 'ya'yan majalisar ne suka amince da bukatar bayan mataimakin shugaban masu rinjaye Sanata Bala Na'Allah ya gabatar da kudurin, inda ya ce la'akari da bukatar ta gaggawa ce da kuma rashin isashen lokaci, ya zama dole 'yan majalisar su amince da ita. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China