Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour, ya shedawa 'yan jaridu cewa, tuni aka riga aka sanar da ma'aikatar harkokin waje da hukumar binciken sirri da hukumomin tsaro da sojoji game da yin garkuwa da wannan bafaranshe.
Ya kara da cewa, kasar Sudan tana cigaba da tuntubar hukumomin kasar Faransa da abin ya shafa, kamar hukumar tsaron kasar Faransar, da kuma gwamnatin kasar Chadi ta hanyar tuntubar jakadun kasashen domin gano mutumin da aka yi garkuwa da shi.
Babban jami'in tsaron kasar Chadi Ahmed Mohammed Bashir, ya fada tun da farko cewa, an kame wannan bafaranshe ne a wani kamfanin hakar ma'adanai inda aka yi garkuwa da shi zuwa wani waje dake da tazarar kilomita 200 a kudancin birnin Abeche dake kasar Chadin a ranar Alhamis data gabata kafin daga bisani aka tusa keyarsa zuwa kasar Sudan.(Ahmad Fagam)