Cibiyar yada labarai ta kasar SMC, ta rawaito Ministan yada labaran kasar Sudan Ahmed Bilal Osman, yana cewa, ana fata kungiyoyin 'yan tawayen da bangaren gwamnatin kasar zasu zauna a teburin sulhu domin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar.
Bilal ya jaddada aniyar gwamnatin Sudan wajen amincewa da shiga yarjejeniyar da bangarorin 'yan tawayen na (SPLM)/arewaci da kuma na yankin Darfur bisa ka'idojin da yarjejeniyar ta tanada.
Dama dai tun a watan Maris na shekarar 2016 ne, gwamnatin Sudan ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a matsayin share fage da kungiyar tarayyar Afrika AU ta gabatar, wanda ake fatar zai tabbatar da shirin tsagaita bude wuta a kudancin Kordofan, da tekun Nile da yankin Darfur, wanda zai bada damar shiga shirin tattaunawar zaman lafiyar tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kasar domin samun dawwamammen zaman lafiya wanda aka tsara tattaunawar a halin yanzu a Khartoum.