in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sudan ta soki gargadin da Amurka ta yi game da shiga kasar
2017-04-01 12:42:46 cri
Gwamnatin Sudan ta soki gargadin da Amurka ta yi wa al'ummarta, kan zuwa kasar saboda barazanar tsaro, tana mai cewa gargadin ba shi da kwakwaran hujja.

Cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen Sudan ya fitar a jiya Jumma'a, gwamnatin kasar ta nesanta kanta da gargadin, wanda ta ce bai yi la'akari da muhimman ci gaba da sauye-sauyen da kasar ta samu ba.

Sanarwar ta ce gargadin ya sabawa rahotonin da MDD da kungiyar Tarayyar Afrika da ta kawancen kasashen Larabawa suka fitar, wanda ya tabbatar da samun tsaro da kwanciyar hankali a yankunan Dafur da Kordofan ta kudu da kuma Blue Nile.

Ta kara da cewa, ikirarin ayyukan ta'addanci da gargadin ya yi, ya sabawa yabon da shugaban hukumar leken asiri ta Amurka CIA da sauran manyan jami'an Amurka suka yi, game da kokari da hadin kai da ta Sudan din ta bayar wajen yaki da ayyukan ta'addanci da masu tsatssauran ra'ayi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China