in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihohin yankin Darfur za su cigaba da zama yadda suke
2016-04-24 13:26:59 cri
A jiya Asabar ne kwamitin shirya kuri'ar raba gardama a yankin Darfur na Sudan ya shelanta a birnin Khartoum hedkwatar kasar cewa, bisa sakamakon da aka samu ta hanyar jefar kuri'ar raba gardama, an ce, masu kada kuri'a sama da kashi 97 cikin dari sun nuna goyon baya ga cigaba da kasancewar jihohin yankin Darfur a rarrabe kamar yadda suke a yanzu, wato jihohi biyar.

Shugaban kwamitin ya bayyana a taron manema labaru cewa, kimanin mutane miliyan 3.08 sun kada kuri'ar amincewa, wadanda suka dau kashi 97.72 cikin 100 na baki dayan masu jefa kuri'ar.

Bisa shirin kuri'ar raba gardama da gwamnatin Sudan ta shirya, an ce, idan masu kada kuri'a su nuna goyon baya domin hadewa wadannan jihohi biyar zuwa babban yanki guda, za a kafa wani kwamitin kundin tsarin mulki mai zaman kansa, domin kulawa da yankin Darfur baki daya. Amma idan jama'ar su ki amincewa da hada su, za a ci gaba da kasancewa kamar yadda ake a yanzu, kuma za a wargaza hukumar rikon kwarya dake kulawa da yankin a halin yanzu.

A watan Oktoban bara ne, shugaban kasar Sudan Omar Hassan Ahmad Al-Bashir ya shelanta cewa, gwamnatin kasar za ta shirya kuri'ar raba gardama a yankin Darfur a watan Afrilun bana, domin yanke shawarar ko za a hada wadannan jihohi biyar zuwa wani babban yanki mai zaman kansa ko a'a.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China